Bayan gwamnatin Ghana ta yi nasarar samun bashin dala biliya uku da hukumar lamuni ta duniya IMF, manzarta a kan harkokin kudi da tattalin arziki a kasar na tsokaci a kan makomar wannan bashi da aka ciyo, yayin da wasu ke dora ayar tambaya a kan yarjejeniyar bada bashin.
Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo, Cif Emmanuel Iwuanyanwu ya sake rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saki Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB.
Cibiyar kula da harkokin tattalin arziki ta bayyana damuwarta game da maimaita kura-kurai da gwamnatoci suka yi a baya wanda ya sanya tattalin arzikin Ghana ya tabarbare tsawon shekaru.
An ayyana jihohin Ondo, Bayelsa da Legas a matsayin inda aka fi tsananin fama da tsadar kayayyaki a Najeriya a cikin watan Maris na wannan shekara.
Jagororin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da aka ayyana a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasar sun soma maida martani ga al'ummomin kasa-da-kasa kan takaddama da cece-kucen da suka biyo bayan ayyana Tinubun a matsayin zababben shugaban kasa.
A karshe ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da mutane 85 a kauyen Wanzamai da ke cikin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara sun amince su karbi Naira 20,000 kan duk wadanda aka sacen.
Yau Litinin ake shirin kammala bukukuwan Ista da Kiristocin duniya ke yi na tuna da daya daga cikin tushen imanin Kirista: mutuwar Yesu da kuma tashinsa daga matattu, bikin da aka dauka babban al’amari a Ghana, inda Kiristoci ke shirya yadda za su gudanar da wadannan ranakun Ista masu muhimmanci.
Domin Kari