Yayin da zabukan gwamnoni da 'yan Majalisun Jihohi ke kara karatowa, an yi kira ga al'ummomin jihohin Adamawa da Taraba da su fito sosai don zabar nagargaru.
An yi kira ga al'ummar Kirista, musamman ma matasa, da su gudanar da shagulgulan Ista ta hanyar da ta dace da koyarwar addinin Kirista a maimakon masha'a da sauran bidi'o'i.
Paparoma Francis ya yi bukin Ista (Easter) tare da yin addu'a ga masu fuskantar tsanani a sassan duniya
Yayin da duniya da masu saka ido a ciki da wajen Najeriya ke bayyana zaben da Najeriya ta gudanar kwanan nan a zaman mai inganci kuma na tarihi
Yayin da ake cigaba da tsokaci kan irin gwamnatin da Shugaban Najeriya mai barin gado Janar Muhammadu Buhari zai kafa, kungiyoyin Fulani da na matasa na kirfan 'yan Najeriya su ba shi hadin kai da kuma lokaci.
Yayin da zabukan gwamnoni da 'yan Majalisun Dokokin jihohi ke kara karatowa, 'yan jam'iyyar APC a jihar Katsina na korafin wasu matakan da gwamna Ibrahim Shehu Shema dan Jam'iyyar PDP ke daukawa a jihar Katsina, wadanda su ka ce na yaudara ne.
Janar Buhari ya ce a zabi APC sak a zabukan da ke tafe. Ya karyata 'yan PDP masu cewa ya amince a zabe shi.
Shugaban Hukmar Zaben Najeriya Furfesa Attahiru Jega ya yaba ma Kwamishinan Zaben Jihar Kano, marigayi Mika'ilu Abdullahi
A wani al'amari mai ban sha'awa da mamaki, kankana ta taimaka da wanke hannaye masu kaushi da tauri ko kuma dauda, har na'urar tantance masu kada kuri'a ta iya tantancewa
Wani soja dauke da makami
Yayin da sakamakon zaben shugaban kasa da na majalisun dattawa da na wakilai ke kara fitowa a hukumance, jam'iyyar APC na dada galaba a yankin kudu maso yammacin Najeriya
Sakamakon da ke fitowa daga jihar Adamawa na nuna cewa dan takarar shugabancin Najeriya na APC, Janar Muhammadu Buhari (murabus) shi ke kan gaba.
Yayin da Shugaban Najeriya ya samu kuri'u mafi yawa a jihar Nasarawa, jam'iyyar adawa ta APC ta samu kujerun sanata biyu daga cikin ukun.
Babbar jam'iyyar adawa ta APC ta yi gagarumar nasara a jihar Oyo, inda ta cinye zabukan Shugaban kasa da na Sanatoci da kuma 12 daga cikin 14 na 'yan Majalisar Wakilai.
Domin Kari