Alhazan jihar Kano da suka biya aikin hajjin bana ta hanyar asusun adashen gata suna zargin hukumar alhazai ta jihar da rashin cika alkawarin cewa sune rukunin farko da za’a baiwa fifiko a yayin raba kujerun aikin hajjin bana.
Kimanin dalibai dubu 15 daga makarantun gwamnatin jihar Kano ba sa cikin jerin daliban dake rubuta jarabawar NECO da aka fara yau saboda takaddamar kudi tsakanin gwamnatin jihar da hukumar ta NECO.
Yan Najeriya, musamman manoma da mamallaka kamfanoni da masana’antu na ci gaba da bayyana damuwa akan hauhawar farashin man dizal, da ke haifar da tsadar safarar kayayyaki zuwa bangarori daban daban na kasar.
Kungiyar masu masana’antu ta Najeriya tace hauhawar farashin kayayyaki da tsadar aikace-aikace da ake fama da su a kasar na tilastawa wasu daga cikin ‘yayanta rufewa kamfanonin su.
Kamfanin zirga zirgar jiragen sama na Azman Air ya mayar da martani ga yunkurin gwamnatin jihar Kano na kin amincewa da kamfanin domin jigilar alhazan jihar kamar yadda hukumar kula ayyukan hajji ta Najeriya ta sahhale.
Wani lauya mai zaman kansa a Kano ya gurfanar da gwamnan Kano gaban babbar kotun Kano, yana kalubalantar tsarin gwamnatin jihar na haramtawa mutane fita daga karfe 7 zuwa 10 na safiyar ranar Asabar din karshen kowanne wata.
Kungiyoyin kasa da kasa dake gwagwarmayar kare ‘yancin dan Adam da wadanda ke ayyukan wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umar Nahiyar Afrika da na sassan duniya, sun gudanar da taro kan zaman lafiya da kuma martaba hakkin bil’adama a Kano.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda zaben zai kaya da kuma bangaren da ‘yan takarar za su karkata domin neman kuri’a.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya na daukar matakan da suka dace domin wadata rundunar sojojin saman Najeriya da kayayyakin aiki na zamani, inda ya bukaci jami’an rundunar su kara kaimi wajen murkushe ayyukan ta’addanci a sassan kasar.
Hukumomin kula da Asibitin koyarwa na Aminu Kano, sun yi karin haske dangane da dalilan karin kashi dari bisa dari na kudaden aikace-aikace ga marasa lafiyar dake ziyartar asibitin.
Masana dokokin kasa da masu sharhi akan harkokin siyasar Najeriya sun fara mahawara game da batun janye takara da wasu ministocin shugaba Muhammadu Buhari suka yi da kuma sahihancin komawa su ci gaba da rike mukaman su.
Ma’aikatar ayyukan jinkai da bada agajin gaggawa ta Najeriya na gudanar da taron bada horo kan sana’o’in hannu da noman kifi ga Nakasassu maza da mata da suka fito daga shiyyar arewa maso yammacin kasar, a wani mataki na karfafa musu gwiwa su dogaro da kai
Yayin da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fayyace dalilan da suka karfafa masa gwiwa wajen zabar mataimakin sa Nasiru Yusuf Gawuna ya gaje shi a kujerar gwamna, ‘ya'yan Jam’iyyar APC a jihar na bayyana mabanbantan ra’ayi dangane da matakin gwamnan.
Domin Kari