Mawakiyar Najeriya Tems ta baiwa masoyanta mamaki ta hanyar gayyatar Wizkid da Justin Bieber, domin su hau dandamali su rera shahararriyar wakar ta mai suna Essence.
Ali Nuhu ya bayyana tarihin rayuwarsa da kuma irin gwagwarmayar da ya sha, wadda ta kai shi ga samun gagarumar nasara a masana’antar shirya fina-finai.
A wani kokari na tunawa da ‘yan mata daliban Najeriya da har kawo yanzu ba’a gan su ba, bayan sace su da mayakan Boko Haram suka yi a Chibok, an haska wani fim mai suna “Statues Also Breathe, ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu a birnin Legas.
Kwanan nan ne shahararren tauraro a masana’antar Adam A. Zango, ya fito yana bayanin irin matsalolin damuwa da yake fuskanta, lamarin da ya fallasa zahirin irin matsalolin da fitattun mutane a idon duniya ke fuskanta.
Kungiyar ninkaya zuwa kasan ruwa ta mata ta Scuba tana hada hancin mata a dukan matakan shekaru, da yare har ma da kabila, kan turba daya ta sha’awar shawagi a karkashin ruwa.
Shekara goma bayan da mayakan Boko Haram a Najeriya suka sace ‘yan matan makarantar Chibok fiye da 270, har yanzu 82 ba su samu kubuta ba; Masu fafutukar kare muhalli da ‘yan cin 'dan Adam sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dakatar da ayyukan kasuwancin Shell a Niger Delta, da wasu rahotanni
Hukumar ta ce matakin haramta fina-finan ya biyo ne bayan damuwar da al’umma ke da ita, na yiwuwar yin mummunan tasiri ga matasa masu tasowa, da kuma wargaza kyawawan dabi’u.
A ranar Talata, 9 ga watan Afrilu ne masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood a Najeriya ta girgiza da babban rashin daya daga cikin jarumanta. Saratu Gidado da aka fi sani da Daso ta rasu ne a Kano bayan ta yi sahur na ranar karshe ta azumin watan Ramadan ta koma barci.
Domin Kari