Mun ji ta bakin wasu a jihar Kano inda masu kasuwancin gurasa suka yi zanga-zanga a kan tsadar kaya a Najeriya; Yayin da kasashen Afirka ke ci gaba da fafatawa a gasar AFCON, wata karamar gasar ta kwaikwayon AFCON ta na gudana a birnin Jos na Najeriya, da wasu rahotanni
Karin haske akan ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkino Faso daga kungiyar ECOWAS; Tsohon shigaban Amurka Donald Trump, wanda bisa dukkan alamu zai zama 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican, ya fara barazanar dakile wata yarjejeniyar gwamnatin Biden, da wasu rahotanni
Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya yi tsokaci a game da tasirin sashin Hausa na Muryar Amurka.
A ci gaba da shagulgulan cikar VOA Hausa shekara 45 da kafuwa, ma’aikatan shashin a Washinton DC sun gudanar da ‘yar kwarya-kwaryar liyafa, wacce ta samu halartar baki daga Amurka da wakilan ofishin jakadancin Najeriya a Washington.
Ministan Zongo a Ghana, Ben Abdallah Banda ya tsokaci a game da cikar Muryar Amurka shekara 45 da kafuwa.
A Yamai na jamhoriyar Nijar, Abdourahamane Mai Hula, wanda ya ke cikin masu sauraren sashin Hausa na Muryar Amurka tun lokacin da aka bude shashin shekaru 45 da suka gabata, ya yi tsokaci game da cikar Muryar Amurka shekara 45 da kafuwa.
Duk da matakai da ake cewa ana dauka don samar da tsaro, ana ci gaba da samun matsalar satar mutane don kudin fansa a wasu sassan kasar, ciki har da Abuja babban birnin tarayyar kasar.
Alexander Novak, wanda ke kula da sashen makamashi na Rasha ya ce, "Babban abokan hulda a halin da ake ciki yanzu su ne China, wadda kasonta ya karu da kusan kashi 45% zuwa 50%, sai kuma Indiya."
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce ba ta gamsu cewa sojojin Najeriya za su gudanar da irin bincike na gaskiya ba a game da harin da sojoji suka kai a kauyen Tudun Biri a Kaduna, wanda ya halaka sama da fararen hula 100.
Domin Kari