Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mobile World Congress Americas

12-14 September 2017 San Francisco, CA, USA

VOA Hausa @ MWC Americas

Ku kasance da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Ibrahim Jarmai da zai rika aiko da rahotanni daga taron baje kolin harkokin aikawa da sakonnin tafi da gidanka na kasashen duniya da ake gudanarwa a birnin San Francisco, inda sama da masu baje koli dubu daya suke halarta, da kuma wakilai daga Amurka ta arewa, da tsakiya da kuma kudanci. Mahalarta taron zasu baje kolin fasaha ta zamani da kuma sababbin hanyoyin sadarwa na baya bayan nan da aka kirkiro, inda aka bada karfi ainun kan cibiyar fasahar sadarwar zamani Silicon Valley, da sababbin hanyoyin sadarwa da wasanni da makamantan haka. Duk abinda kake nema da ya jibinci hanyoyin sadarwar tafi da gidanka, zaka same su a taron MWC Americas 2017.

Ibrahim Jarmai
Ibrahim Jarmai

XS
SM
MD
LG