Wadanda za a sakin sun hada da, mutane 445 daga zirin Gaza da aka kama bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya haddasa yakin, 60 daga cikinsu na zaman gidan kaso na dogayen shekaru da 50 da aka yankewa daurin rai da rai, da 47 da aka sake kamawa bayan musayar fursunonin 2011