Biyo bayan kalaman da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi jim kadan bayan rantsuwar kama aiki na mayar da birnin kan taswirarta na asali, wasu masu kananan sana’o’i na neman a yi nazari kar a jefa su cikin matsin rayuwa.
Tashin farashin dala a Najeriya ya sa kayayyaki musamman na masarufi sun yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya jefa al'umar kasar cikin halin ni-'yasu.
Daga cikin bukatun da kungiyar ta NLC ta gabatar, akwai neman a kara mafi karancin albashin ma’aikata.
Yayin da damina ke kankama a sassan Najeriya, Kungiyar Manoman shinkafa, sarrafa ta da kuma kasuwancinta ta Najeriya ta kaddamar da Shirin ta na bada lamunin kayan noma na musamman domin karfafa gwiwar manoma.
Kungiyar Tarayyar Turai ta ci tarar Meta, babban kamfanin da ya mallaki Facebook, dala biliyan 1.3 tare da umartarsa da ya daina mika bayanan masu amfani da shafin zuwa Amurka nan da watan Oktoba.
Sai dai kungiyar Malaman jami'a ta ASUU ba ta ji dadi ba, ganin yadda aka cire su cikin wadanda za su ci moriyar wannan kari.
Cibiyar kula da harkokin tattalin arziki ta bayyana damuwarta game da maimaita kura-kurai da gwamnatoci suka yi a baya wanda ya sanya tattalin arzikin Ghana ya tabarbare tsawon shekaru.
Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce matsalar yunwa na ci gaba da karuwa a yankin Yammacin nahiyar Afirka.
Domin Kari
No media source currently available
Mun ji ta bakin Bode Gbadebo, wani 'dan jarida kuma mai sharhi a Najeriya, akan wani bangare na jawabin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a taron UNGA
Bayani kan yadda shugabannin kasashen duniya suka gabatar da jawabai da suka tabo batutuwa daban-daban a wurin babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da ya gudana a birnin New York na Amurka
To a game da wannan babban taron na Majalisar Dinkin Duniya, mun samu rahotanni kai tsaye daga birnin New York yadda aka gudanar da taron
A babban taron majalisar dinkin duniya da ya gudana a nan Amurka, shugabannin kasashen duniya sun sanar da takwarorinsu matsaloli da kuma manufofinsu, mun tambayi Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, na Jami’ar Abuja, dalilin da ya sa manufofin da ake cimmawa a wajen irin wannan taro, ba sa kai labari
Mun tambayi Farfesa Bello Muhammad Badah na jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto a Najeriya ko me wannan hukunci na kotun kararrakin zabe a Kano ke nunawa.
Muryar Amurka ta tattauna da wani mai fafutuka da sharhi a Najeriya, Nastura Ashir Sharif ta Skype, inda muka ji ra’ayin shi a game da tallafin rage radadin a wannan lokaci.