Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Romney Ya Zabi Wakili Paul Ryan Dan Takarar Mataimakin Shugaban kasa


Tsohon Gwamnan jihar Massachusetts, Mitt Romney da uwargidansa Anne suke gaida magoya bayansa a wani yakin neman zabe.
Dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican Mitt Romney ya zabi dan majalisar wakilan Amurka Paul Ryan ya zama mutuminda zai zame masa mataimakin shugaban kasa a yakin neman zaben kujerar da ake yi domin zabenkasa da za a yi cikin watan Nuwamban bana.
Tsohon gwamnan Massachusetts Mitt Romney, yake yakin neman zabe a jihar Ohio.
Tsohon gwamnan Massachusetts Mitt Romney, yake yakin neman zabe a jihar Ohio.

Yau Asabar Romney yayi wan nan sanarwar a wani gungun taron magoya bayansa a doron wani tsohon jirgin ruwan Amurka da ake kira USS Wisconsin a jihar Virgina dake gabashin Amurka.
Dan takarar da sabon mutuminda ya dauka sun bayyana tare a fara yakin neman zabe na kwana hudu da zasu yi mota.
Dan shekaru 42 da haifuwa Ryan ya dade a majalisa inda yake wakiltar jihar Wisconsin dake tsakiya maso yammacin Amurka, kuma yana samun goyon bayan rikakkun masu ra’ayin mazan jiya anan Amurka.Shine shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisa, kuma shine jagoran masu neman rage gibin kasafin kudi ta wajen rage kudade da gwamnati take kashewa.
XS
SM
MD
LG