Accessibility links

Girgizar Kasa A Iran Ta Halaka Fiyeda Mutane 80, Daruruwa Kuma Sun Jikkata


Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad
Jami’ai a Iran sun ce akalla mutane 80 ne suka halaka sakamakon wasu girgizar kasa biyu masu karfi arewacin kasar, kusa da birnin Tabriz.
Bututun man kasar Iran
Bututun man kasar Iran

Masana yanayin karkashin kasa sun sami sabanin kan hakikanin karfin girgizar,amma jami’ar Tehran da kuma hukumar kula da yanayi a karkashin kasa ta Amurka duk sun ce karfin girgizar ya kai shida ku fi.

Jami’an kasar suka ce girgizar sunyi barna ga kauyuka kusa da Tabriz, da haddasa mace mace masu yawa daruruwan mutane kuma sun jikkata.
XS
SM
MD
LG