Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ecuador Ta Baiwa Julius Assange Mafaka.


Hotun Julian Assange Mutuminda ya kafa dandalin WikiLeaks, mai fallasa sirrin gwamnati da kungiyoyi.
Alhamis din nan ne ministan harkokin wajen Ecuador, Ricardo Patino, ya bada sanarwar haka a Quino, yana mai cewa lafiya da tsaron Assange yana cikin hadari. Yace ba za a yiwa Assange adalci ba idan aka mikashi hanun Amurka.

Ministan harkokin wajen Britaniya William Hague, yace Ingila ba zata baiwa Assange damar barin kasar ba, kuma a shirye take wajen ganin ta mika shi ga kasar Sweden.
'Yansandan Ingila a ofishin jakadancin Ecuador dake kasar.
'Yansandan Ingila a ofishin jakadancin Ecuador dake kasar.

Mahukuntan Sweden suna neman Assange saboda ya amsa tambayoyi kan zargin ya tilastawa wata mace lalata da shi. Assange ya musanta wan nan zargi.
Bayanda Ecuador ta yanke wannan shawara, Sweden ta gayyaci jakadan Ecuador dake kasar, a wani mataki na difilomasiyya. kakakin gwamnatin Sweden yace gwamnatin kasar “ba zata lamunta ba” ganin Ecuador tana kokarin katsalandan cikin harkokin shari’ar kasar.

Daya daga cikin lauyoyin Assange, yayi kira ga mai gabatar da kara na Sweden yazo London ya yiwa Assange tambayoyi, ganin yanzu babu sauran zarafin mutuminda yake baiwa kariya zai je Sweden, saboda yanzu an bashi mafaka.

Assange yana cikin ofishin jakdancin Ecuador tun cikin watan Yuni, bayanda ya sha kaye a kotu a kokarinsa na hana hukumomin kasar mika shi ga hukumomin Sweden.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG