Accessibility links

Ana Fargabar hatsarin Jirgin Ruwa A Guinea Ya Halaka Mutane Da Dama

  • Aliyu Imam

Masu aikin ceto, a hatsarin jirgin ruwa a kasar Guinea.
Ana fargabar mutane masu yawa ne suka halaka lokacinda wani jirgin ruwa ya nutse kusa da gabar tekun kasar Guinea.
Yau Asabar jami’an kasar suka ce an tabbatarda mutuwar mutane takwas ciki harda yara biyu.

Masu bincike suka ce kimanin mutane 50 ne suke cikin jirgin ruwa jiya jumma’a bayan tashin jirgin daga babban birnin kasar Conakry zuwa wani tsibiri mai ‘yar tazara daga gabar tekun a Afirka ta yamma.

An ceto wasu daga cikin fasinjoji dake cikin jirgin, amma anji wani jami’in aikin ceto yana
cewa sun fara fidda tsammanin ceto karin mutane da rai, ma’ana kimanin mutane 30 sun halaka kenan.
Babu bayani kan musabbabin wannan hadari.
XS
SM
MD
LG