Accessibility links

An Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Ma'aikatan Hakar Ma'adinai Na Afirka Ta Kudu?


Iyalai da ma'aikatan hakar ma'adinai suka hallara kan wani tudu kusa da inda 'Yansanda suka kashe 'yan uwansu
Bayan da ‘Yansanda suka harbe suka kashe ma’aikata 34 lokacinda ma’aikata suke zanga zangar yajin aiki.

Duk da haka, wasu muhimman kungiyoyin kwadago da wasu mahaka sun ki su sa hanu kan wannan yarjejeniya.
'Yan makoki suke dauke da akwatin gawar daya daga cikin ma'aikata 34 da 'Yansanda suka kashe
'Yan makoki suke dauke da akwatin gawar daya daga cikin ma'aikata 34 da 'Yansanda suka kashe

A cikin watan jiya ne ma’aikatan hakar ma’adinan suka fara yajin aiki, wadda ya janyo fargaba kan yadda yajin aikin zai shafi banagaren hakar ma’dinai a kasar mai riba.

An kulla yarjejeniyar sulhun ne da nufin share fage domin a fara tattaunawa kan rikicin karin albashi tsakanin kamfanin hakar ma’adinai na uku a girma a duk fadin duniya, da ma’aikatansa.

A safiyar Alhamis din nan ne kamfanin Lonmin, da babbar kungiyar ma’aikatan hakar ma’adinai ta Afirka ta kudu, suka sanya hanu kan yarjejeniyar.

Amma kungiyar ma’ikatan hakar ma’adinai da birkiloli ta kasar, tayi watsi da yarjejeniyar, tana zargin kungiyar da ta sanya hanu kan yarjejeniyar cewa ‘yar barandan gwamnati ce.
XS
SM
MD
LG