Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Amurkawa Suna Fama Da Talauci, Inji Hukumar Kidaya.


Kungiyoyin tallafi a Amurka suke fama da karuwar mutane da suke fadawa talauci.
Wani sabon binciken da gwamnatin kasar Amurka ta gudanar ya nuna cewa a shekarar 2011, a cikin mutane 7 kowane daya ya yi fama da radadin talauci a nan Amurka.

Kwararrun masanan hukumar kidayar jama’a ta Amurka sun bayyana ma’anar talauci da cewa samun albashin da ba kai dola dubu 23 da 21 ba a gidan da ke da mutum hudu.

Binciken ya nuna cewa Amurkawa miliyan 46 da dubu dari biyu na cikin talauci.

Masanin cibiyar Brookings, Ron Haskings ya ce ana fama da nacin talaucin ne saboda rashin ayyukan yi, kuma ya ce ba a kirkiro ayyukan yin da saurin da ya kamata a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke farfadowa daga komada mafi munin da aka gani a cikin shekaru da dama.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG