Accessibility links

Libya Ta Kama Mutane Hudu Dangane Da Harin Da Aka Kai Ofishin Jakadancin Amurka.


Masu zanga zanga da ta yi sanadiyyar mutuwar jakadan Amurka A Libya
Jami’an Libya suka ce hukumomin kasar sun kama mutane hudu dangane da mummunar tarzomar da aka yi cikin makon nan kan karamin ofishin jakadancin Amurka dake Benghazi, a dai dai wannan lokacin ne kuma hukumomi suke shirin fuskanatar karin tarzoma a fadin gabas ta tsakiya, saboda wani silima na batunci kan musulunci.

Hukumomin Libya basu bada karin bayani kan mutanen hudu da aka kama dangane harin da aka kai ranar talata wadda yayi sanadiyyar mutuwar jakada Christopher Stevens, da wasu jami’ai uku.

Hukumomin leken asirin Amurka suna binciken zargin da hanun magoya bayan kungiyar al-Qaida a kai wannan hari. Duk da haka suka ce basu da wani sheda mai karfi kan wannan zargi.

Ahalinda ake ciki kuma, an kashe ‘yan zanga zanga hudu a Yemen, lokacind a wani gungun jama’a suka farwa ofishin jakdancin Amurka a jiya Alhamis.
XS
SM
MD
LG