Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mitt Romney Yana Kokarin Sake Karkato Yakin Neman Zaben Shugabancin Amurka Da Yake Yi Ya Mike Bayan.....


Mitt Romney mutuminda yake takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Republican.
Dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican Mitt Romney, yayi kokarin sake karkato yakin neman zaben da yake yi ya dawo kan hanya, bayanda wani fefen vidiyo da aka dauka a sirce, ya kufularda magoya bayan shugaba Obama sosai.
Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Mitt Romney da uwargidansa Ann Romney.
Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Mitt Romney da uwargidansa Ann Romney.

Anji Mr. Romney cikin vidiyon yana cewa kashi 47 cikin dari na masu zabe a Amurka masu goyon bayan shugaba Obama basa biyan haraji, kuma sun dage hakkinsu ne a basu inshoran kiwon lafiya da wasu kayan more rayuwa ba tareda sun dauki nauyin hakkinda ya rataya a wuyarsu ba.

Jiya talata Mr. Romney ya amince bai tsara maganar da yayi da kyau ba, duk da haka yace zai ci gaba da yakin neman ganin an rage karfin da girman gwamnatin tarayyar Amurka.

Kakakin fadar White House Jay Carney yace shugaba Obama, baya kallaon mutane da suke samun tallafin gwamnati kamar dalibai a matsayin mutane da aka “zalunata ba”.
XS
SM
MD
LG