Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Hakar Ma'adinai A Afirka Ta kudu Zasu Koma Aiki Gobe Alhamis.


Taron ma'aikatan hakar ma'adinai suke gangamai a wani babban filin wasanni.
Kungiyar kwadago ta ma’aikatan hakar ma’dinai a Afirka ta kudu ta sanya hanu kan yarjejeniya da masu kamfanonin hakar ma’adinai, domin kawo karshen mummunar yajin aiki da zanga zanga na tsawon mako biyar, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar ma’aikata 45.

Masu aikin hakar ma’adinai sun hallara wani dandalin wasani a yammacin jiya talata suka fara sowa da raye raye bayanda suka sami labarin an cimma yarjejeniya. Saboda haka sun shirya komawa bakin aiki gobe Alhamis idan allah ya kaimu.
Masu aikin hakar ma'adinai suke maci a Afirka ta kudu.
Masu aikin hakar ma'adinai suke maci a Afirka ta kudu.

Ma’aikatan kamfanin hakar ma’adinai da ake kira Lonmin, zasu sami karin albashi na kashi 22 cikin dari kasa da abinda suka nema, sannan kuma za a biya su dala dari biyu da hamsin diyyar lokaci da basu yi aiki ba.

Ranar 16 ga watan Agusta ne ‘Yansanda suka bude wuta kan masu zanga zanga a harabar hakar ma’adinai. Amma tarzomar ta kada al’umar kasar baki daya.
XS
SM
MD
LG