Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Guinea-Bissau na Zargin Kasar Portugal


Carlos Gomes Junior ke jawabi ga magoya bayansa yayin da ya ke takarar Shugaban kasa na jamiyya mai mulkin Guinea-Bissau
Carlos Gomes Junior ke jawabi ga magoya bayansa yayin da ya ke takarar Shugaban kasa na jamiyya mai mulkin Guinea-Bissau
Gwamnatin Guinea-Bissau na zargin kasar Portugal da goyon bayan wani yinkurin mata juyin mulki, bayan wani mummunan harin da aka kai kan sojoji a babban birnin kasar.

Wannan harin da aka kai da asubahin jiya Lahadi kan wani barikin sojoji ya hallaka mutane akalla 6. Wani mai magana da yawun gwamnati ya ce an kai harin ne bisa jagorancin Keftin Pansa N’tchama, wanda ke da alaka da jami’an sojin da ke goyon bayan tsohon Firayim Minista Carlos Gomes Junior.

Gomes ya ci zagaye na daya na zaben shugaban kasar Guinea-Bissau da aka gudanar a farkon wannan shekarar, to amman wani juyin mulkin da aka kaddamar a watan Afirilu ya tsai da zaben.

Mai magana da yawun gwamnatin, Fernando Vaz, y ace kwanan nan N’tchama ya dawo daga kasar Portugal, wadda ta yi wa Guinea-Bissau mulkin mallaka.

Wani jawabin da gwamnatin Portugal ta yi yau Litini ya yi kiran da akai zuciya nesa a Guinea-Bisaau amman bai ambaci zargin ba.

Guinea-Bissau dai ta jure wa dadadden tashin hankali tun bayan da ta sami ‘yancin kai a 1974.

Kasar ta sha ganin juye-juyen mulki da yunkurin juyin mulki, wanda mafi munin ciki shi ne na hallaka Shugaba Joao Bernardo Vieria a 2009. Ana zargin N’tchama da taka rawa a wannan kisan.
XS
SM
MD
LG