Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaka Ma'adanan Afirka ta Kudu


Mahaka ma'adanan Afirka ta Kudu na sauraron jawabi daga shugabanninsu.
Kamfanonin hakar zinari na Afirka ta Kudu sun rattaba hannu kan sabuwar yarjajjeniyar albashi da zummar kawo karshen yajin aikin da ya durkusar da kamfanonin.

Yarjajjeniyar da aka cimma tsakanin kungiyar mahaka ma’adanai da kuma manyan kamfanonin hakar ma’adanai uku, da aka rattaba hannu akai a yau dinnan Alhamis, ta tanaji ariya din karin karin albashi na tsakanin kashi 11% zuwa 20%.

Wannan karin ya biyo bayan wani karin da aka yi tun a watan Yuni.

Yajin aiki ba bisa ka’ida ba da mahaka ma’adanan Afirka ta Kudu su ka shiga yi ya tsananta tun a watan Agusta, yayin da ‘yan sanda su ka bude wuta kan masu yajin aiki a kamfanin hako karfen platinum har su ka kashe mutane 34. ‘Yan sandan sun ce sun yi harbin ne don kare kansu.

Daga bisani dai ma’aikatan wannan kamfanin hako ma’adanan sun sami karin albashi da kashi 22%, wanda hakan ya sa ma’aikatan sauran kamfanonin hako ma’adanan su ma su ka zaburo don bukatar karin albashi da kyautata yanayin aiki.

Wannan yaje-yajen aikin ya sa kamfanonin hako ma’adanai sun bayar da wa’adin komawa bakin aiki ko kuma ma’aikatan sun fuskanci kora.

Yarjajjeniyar ta yau Alhamis ba ta shafi ma’aikatan kamfanonin hako karfen platinum da gawayin kol ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG