Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauye-sauye a Dokar Mallakar Filaye a Afirka


Wata gona a Afirka
Taron kasa da kasa na masanan kimiyyar bunkasa halin zaman rayuwar al’umma ya maida hankali kan batun samun filayen noma da ginin gidajen jama’a a nahiyar Afirka a zaman muhimmin abin dubawa.
T
aron yace rashin karfafa daukan matakan bunkasa harkokin noma a nahiyar Afirka ne ke janyo koma bayan tattalin arziki.Babban taron na kasa da kasa da aka gudanar a kasar Kamaru a ranakin bakwai dfa takwas ga wannan watan na Nuwamba yayi kiran da a karfafa fannin kimiyyar sanin fannin kimiyyar noma da labarin kasa, a kuma inganta hanyar samar da filaye ga jama’a domin gudanar da ayyukan noma da gioggina gidaje da masana’antu.

Madiodio Niasse, Darekta na kamfanin ayyukan rarraba filaye a kasar Kamaru, yana muma daga cikin wadanda suka halarci taron ya yi Karin haske.
A ta bakinsa, “Batun mallakar fili yanzu ya zama wani babban batun da kasa da kasa ke baiwa muhimmanci, domin an gano cewa batun mallakar fili imma dai na noma ko ginin gida ko kuma masana’antu idan ba’a bi a hankali bas hike zaman ummul haba’isin tada rikici a mafi yawan kasashen Afirka. "

Darekta Niasse ya kara da cewa, “Yace wani babban dalilin dake janyo hankulan kasa da kasa shine albarkar da kasa ke dashi a fannin noma, ko albarkatun karkashin kasa da kuma jurewa ayyukan masana’antu, shi yasa Afirka ke da martaba a idon duniya.”

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG