Accessibility links

An hallaka Gwamnar Babban Bankin kasar Guinea.

  • Ibrahim Garba

Sugaban kasar Guinea Conakry, Alpha Condé
An kashe Gwamnar Babban Bankin kasar Guinea.

Wasu ‘yan bindiga ne su ka bude wuta kan motar Aissatou Boiro da daren Jumma’a a Conakry, babban birnin kasar. Ita dai Boiro na binciken wani yinkurin ne na wasu manyan gwamnati na wawurar kusan dala miliyan 2 daga Babban bankin kasar.

Wani jami’in gwamanatin Guinea din ya gaya wa Kamfanin Dillancin Laraban Faransa cewa wannan kisan ba wani abu ba ne face wasu jami’in gwamnati ke mayar da martani.
XS
SM
MD
LG