Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Afirka ta amince da shirin kai daukin soja a Mali


Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan a taron kungiyar ECOWAS da ta dau mataki kan Mali
Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan a taron kungiyar ECOWAS da ta dau mataki kan Mali
Kungiyar Tarayyar Afirka ta amince da shirin kai daukin soja, don taimakawa a fatattaki ‘yan bindigar Islama daga arewacin Mali.

Da yake kungiyar Tarayyar Afirka ta amince da hakan a jiya Talata, a yanzu dole ne shirin ya kumi sami amincewar Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya.

Kwamishinan Kwamitin Tabbatar da Zaman Lafiya da Tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka Ramtane Lamara, ya yi kira ga hukumar ta kasa da kasa, da ta bayar da umurni a girke dakarun na tsawon shekara guda a wa’adin farko. Ya ce manufar wannan yinkurin shi ne, a sake kwato arewacin Mali, a wargaza tungayen ta’addanci a kuma maido da ikon gwamnati a fadin kasar ta Mali.

Gwamnatin wuccin gadi ta Mali, ta bukaci gudunmowar dakarun da za su taimaka mata, ta fatattaki ‘yan bindigar Islama da su ka kwace iko da arewacin Mali, bayan wani juyin mulkin da aka yi a watan Maris da zummar hambarar da gwamnati. Kungiyar kasashen yammacin Afirka, ECOWAS a takaice, ta bayar da amincewarta ranar Lahadi na wa’adin tsawon shekara guda ga dakaru 3,000.

Lamamra ya ce ya na ganin Majalisar Dinkin Duniya za ta amince da shawarar kafin karshen wannan shekarar.


Manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Sahel, Romano Prodi, ya fadi jiya Talata cewa har yanzu kwai damar tattaunawa don kawo karshen matsalar amman kuma ya na ganin shirin kai dauki ta fuskar soji din wata hanya ce ta warware wannan matsalar.
XS
SM
MD
LG