Accessibility links

Shugaban Isira'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila ka iya fadada farmakinta

  • Ibrahim Garba

Dakarun Isira'ila
Firayim Ministan Isira’la Benjamin Netanyahu ya ce a shirye Isira’ila ta ke, a ta bakinsa, ta yi gagarimin fadada matakan da ta ke daukawa kan mayakan zirin Gaza da ke karkashin ikon Hamas.

Kalaman na Mr. Netanyahu a yau Lahadi, sun zo ne a daidai lokacin da Isira’la ke tara dubban dakaru a tsawon kan iyakar a sailinda tashin Isra’ila da Falasdinawan ke shiga rana ta 5.

Yau Lahadi ma Isra’ila ta tarwatsa wasu wurare a zirin Gaza, inda ta yi ta kai farmaki daga sama da kuma teku a matsayin martanin wutar rokokin da Falasdinawa ke yi. An hallaka akalla yara 3 a dauki ba dadi na baya bayan nan.

Sojojin Isra’ila sun fadada wuraren da su kai wa hare-haren da safiyar yau Lahadi ta yadda su ka yi ta hadawa da gine-ginen da kafafun yada labaran kasaseh waje ke amfani da su. Hukumomi sun ce akalla ‘yan jarida 3 sun sami raunuka a hare-haren. Isra’ila ta kuma kai hare-haren kan wuraren Hamas.

Ministan Harkokin Wajen Faransa Laurent Fabius ya bar barnin Paris a yau dinnan Lahadi zuwa birnin Qudus don bayar da gudunmowar Faransa wajen samar da zaman lafiya.

Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya William Hague ya gargadi Isara’ila cewa za ta fa rasa goyon bayan duniya muddun ta kaddamar da hari ta kasa kan zirin Gaza.

Jami’an Falasdinawa sun ce ‘yan hallaka ‘yan Gaza akalla 48 tun fara tashin hankalin ranar Laraba. Isra’ila ta ce ‘yan kasarta 3 ne su ka mutu.
XS
SM
MD
LG