Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Morsi Ya Gana da Alkalan Kasar Masar.


Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi tare da sabon babban lauyan gwamnati Talaat Abdullah

Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya gana da majalisar kolin alkalai.

Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi zai gana da majalisar kolin alkalan kasar, a daidai lokacin da su ke kokarin shawo kan shugaban kasar su hana shi tarawa kan shi tulin iko a matakin da ya dauka makon jiya.

Dokar ta takalo zanga-zanga daga bangaren ‘yan hamayya, wadanda su ka ci gaba da yin dirshan a dandalin Tahrir a kwana na hudu a jere a yau litinin, su na neman da lallai sai Mr. Morsi ya sake lale, ya sauya shawara. ‘Yan hamayya da magoya bayan shugaban kasar sun kira tarurrukan gangami daban-daban a birnin a gobe talata.

Dokar da Mr.Morsi ya kafa ta ce duk shawarar da ya yanke ta zauna, ba daukaka kara a kowace kotu kuma ta haramtawa kotunan kasar rusa wani bangaren majalisar dokoki da kuma soke wani daftarin kundin tsarin mulkin da majalisa ke kattabawa. Masu sukan lamiri sun ce Mr.Morsi ya tattarawa kan shi tulin ikon yin kama karya kamar tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak wanda boren jama’a ya kora daga mulki.

Shugaban ya ce dokar ta dan wani takadirin lokaci ce kuma za ta yi aiki har ya zuwa lokacin da za a zabi sabbin ‘yan majalisar dokoki bisa tanadin wani kundin tsarin mulkin da aka yiwa kwaskwarima. Wani kakakin jam’iyar shugaban kasar ta “Freedom and Justice” wadda ke mulki, ya fada a jiya lahadi cewa mai yiwuwa ne dokar za ta yi wata biyu ko kasa da haka, sannan ya bayyana daukan matakin da cewa wani kokari ne na neman tabbatar da dorewar zaman lafiya a kasar Masar.

A nan birnin Washington, D.C, dan majalisar dattaban Amurka mai fada a ji, John McCain ya soki lamirin dokar ta Mr.Morsi wadda ya ce ba za a yarda da ita ba.
XS
SM
MD
LG