Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Argentina Ta Kai Karar Ghana Gaban Kotun Duniya


Jirgin mayakan ruwan Argentina da Ghana ta kama
Jirgin mayakan ruwan Argentina da Ghana ta kama

Argentina ta bukaci wata kotun duniya da ta umarci Ghana ta sakar ma ta jirgin ruwan ta na ARA Libertad da ta kama tun ranar biyu ga watan oktoba

Gwamnatin kasar Argentina ta bukaci wata kotun duniya da ta saka baki, ta umarci hukumomin kasar Ghana su sakar ma ta wani jirgin ta na yaki da su ka kama.

Jirgin ruwan yakin mai suna ARA Libertad wanda mayakan ruwan kasar ke yin atisaye da shi, ya na hannun hukumomin kasar Ghana tun ranar biyu ga watan Octoba lokacin da ta kama shi bisa bukatar wasu masu saka hannun jarin da ke bin Argentina bashin dola miliyan 300.

A yau alhamis gwamnatin kasar Argentina ta gabatar da karar a gaban kotun duniya mai kula da dokokin ruwayen teku, mai cibiya a Hamburg kasar Jamus.

Mai wakiltar gwamnatin Argentina a karar, Susana Cerutti, ta bayar da hujjar cewa bisa tanadin dokar ruwayen teku ta kasa da kasa, jiragen ruwan yaki na da kariya, sannan ta ce yadda Ghana ta rike jirgin ruwan ta hana shi tafiya, wani al’amari ne mai daure kai.

Argentina ta ce an kama jirgin ruwan ne lokacin da ya je Ghana ziyarar aiki.
Tun da aka fara wannan takaddama jirgin ruwan ya na can a tirke a tashar jiragen ruwan Tema ta kasar Ghana.

Argentina ta kwashe akasarin sojojin ta daga cikin jirgin ruwan tun a watan jiya, ta bar babban kwamandan jirgin kawai tare da wasu sojoji 44.
XS
SM
MD
LG