Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen M23 Na Shirin Ficewa Daga Birnin Goma


'Yan tawayen kasar Congo na sintiri a wani titin garin Sake a tazarar kilomita 25 arewa da birnin Goma

'Yan tawayen Congo na shirin fita daga Goma amma ba wata alamar da ta nuna za su yi wata gagarumar janyewa daga yankin

‘Yan tawayen Jamahuriyar Demokradiyar Congo sun shirya ficewa daga birnin Goma na gabashin kasar a yau Jumma’a, amma nan take babu wasu alamu da ke nuna wata gagarumar janyewa daga birnin.

Kungiyar ‘yan tawayen M23 ta ce za ta janye zuwa wani sansani a tazarar kilomita 20 a bayan garin babban birnin lardin mai tarin muhimmanci, amma za su bar sauran sojoji kimanin 100 a filin jirgin saman birnin na Goma.

Kungiyar ‘yan tawayen wadda, ta kama birnin Goma a makon jiya bayan ta fafata da sojojin Congo da na Majalisar Dinkin Duniya masu tsaron zaman lafiya, ta yi amai ta lashe game da alkawarin ta na ficewa daga birnin ranar alhamis bisa yarjejeniyar da aka cimma da shiga tsakanin sauran kasashen yankin.

Kungiyar ta fara tattara nata ya nata ta na ficewa daga sauran yankunan gabashin kasar Jamahuriyar Demokradiyar Congo, amma wakilin Muryar Amurka Gabe Jaselow ya ce ‘yan tawaye da yawa sun kwashi ganima a gidajen mutane a garin Sake, a ranakun laraba da alhamis a lokacin da su ke ficewa daga yankin.

Mutanen da rikicin kasar Congo ya kora daga gidajen su
Mutanen da rikicin kasar Congo ya kora daga gidajen su


Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Congo ya shaidawa Muryar Amurka cewa sun tabbatar an aikata abubuwan keta haddin bil Adama a birnin Goma.

Ranar laraba gwamnatin kasar Jamahuriyar Demokradiyar Congo ta zargi kungiyar ‘yan tawayen M23 da kisan mutum 64 a garin Goma da kuma raunata fararen hula fiye da 220. Ranar alhamis kungiyar M23 ta gabatar da sanarwar musanta zargin.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG