Accessibility links

Masu Kaifin Kishin Islama a Masar Na Gangamin Goyon Bayan Shugaba Morsi

  • Ibrahim Garba

Masu kishin Islama ke gangamin goyon bayan Shugaba Muhammad Morsi a Masar
Dubun dubatan masu goyon bayan Shugaban Masar Mohammed Morsi na gangami a harabar Jami’ar al-Khahira.

Jam’iyyar ‘Yan’uwantakar Islama ta yi kiran da a yi gangami a fadin kasar a yau Asabar don nuna goyon baya ga Shugaba Morsi da kuma daftarin kundin tsarin mulkin da za a yi kuri’ar raba gardama akai.

A halin da ake ciki kuma dubban masu zanga-zanga na cigaba da mamaye Dandalin Tahrir a rana ta 9 don nuna rashin amincewarsu ga shugaba Morsid da kuma daftarin kundin tsarin mulkin.

Kotunan jihohi ma sun shiga yajin aikin da kotunan tarayya su ka fara na adawa da dokar da ta baiwa Mr. Morsi matukar iko. Alkalan jihohi sun ba da sanarwar daina aiki, in banda a muhimman yanayi, sun a masu kira ga Shugaba Morsi ya soke wannan dokar da ta bashi iko fiya ma da bangaren shari’ar kan shi.
XS
SM
MD
LG