Accessibility links

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Zata Tattauna Da 'Yan Tawaye


Shugaban Jamhuriyar Afrika Ta Sakiya Yana Yiwa Jama'a jawabi
Gwamnatin jamhuriyar Afrika ta tsakiya da gamayyar kungiyar ‘yan tawaye dake kara dosar babban birnin kasar, sun amince da zaman tattaunawa farkon watan gobe ba tare da gindaya sharuda ba.

An bada wannan sanarwar ne jiya asabar jim kadan bayanda mazauna garin Bangui dake gabashin babban birnin kasar suka shaidawa Muryar Amurka cewa, mayakan dake kungiyar ‘yan tawaye ta hadin guiwa da ake kira Saleka sun kwace garin Sibut. Daga baya gwamnati ta tabbatar da kwace birnin da cewa, an kwace Sibut wanda yake tazarar kilimita 180 daga Bangui, ba tare da harba bindiga ko sau da ya ba. Ranar jumma’a dakarun gwamnati suka gaza sake kwace garin Bambari dake kusa da Sibut daga hannun ‘yan tawaye.

Ba a sa ranar tattaunawar ba. ‘yan tawaye sun kwace kimanin kashi daya bisa uku na kasar a cikin makonni uku da suka shige.

A halin da ake ciki kuma. Fadar White House ta sanar da shugabannin majalisar dokoki cewa, an tura dakarun sojin Amurka 50 zuwa kasar Chadi dake makwabtaka da jamhuriyar ta tsakiya, domin su taimaka wajen kwashe ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka daga kasar. Sanarwar fadar shugaban kasar tace, an tura sojojin ne domin kare Amurkawa da kuma kaddarorin Amurka idan bukatar haka ta taso.
XS
SM
MD
LG