Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Yi Alwashin Shawo Kan Mallakar Bindiga


Bindigogi a Majalisar Dokokin jahar Oklahoma

Shugaba Obama ya yi alkawarin yin matsin lambar gaggauta samar da sabbin matakan shawo kan mallakar bindigogi a Amurka

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi alkawarin bada cikakken goyon bayan fadar White House ga kokarin neman shan kan rigimar bindiga a nan Amurka.
Mr.Obama ya fada ranar lahadi, a cikin wata tattaunawa da gidan talbijin din NBC a shirin “Meet the Press” cewa harin da aka kai kwanakin baya kan wata makarantar elemantare a jahar Connecticut wanda ya halaka yara ishirin da manya shida, ita ce rana mafi muni a cikin shekaru hudun da ya yi ya na shugabanci.

Shugaban ya ce zai bukaci goyon bayan Amurkawa game da shawarwarin tsananta binciken halin masu neman sayen bindigogi, da haramta sayar da makaman yaki da kuma zungurun harsashai masu karfin tsiya. Mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden ne zai jagoranci ayarin masu tsara dokar da za ta kawo karshen harbin gama gari a Amurka inda ‘yancin mallakar bindiga ke rubuce a cikin kundin tsarin mulki.

Mr.Obama ya ce sabbin matakan shan kan mallakar bindigogi za su janyo cacar baki, amma dole ne Amurka ta duba ta gani ko ta na da karfin halin daukan sabbin matakan yiwa hancin tufka, maimakon ta bari a manta da harin da aka kai kan makaranta. Shugaba Barack Obama ya ci gaba da bayani ya na cewa: “Kenan tambayar da za mu yi ita ce, a hakikanin gaskiya shin ko mun yi kaduwar da ta isa ta hana mu mantawa da abun da ya faru, kamar irin abubuwan da su ka saba faruwa a yi kwana da kwanaki ana magana a kai, kuma a yi watsi da abun a bar maganar. Ba shakka ni dai ba haka na ke jib a. Wannan wani abu ne wanda, ka na ji, ita ce rana mafi muni a shugabanci na. Kuma ba na fata Allah Ya maimaita”.

Amma Mr.Obama ya ce ya na tababa game da kiran da babbar kungiyar kare muradun wadanda su ka mallaki bindigogi a Amurka ta yi cewa a saka masu gadi da bindigogi a duka makarantun gwamnatin da ke cikin kasar Amurka su kusan dubu dari. Mr. Obama ya ci gaba da bayani ya na cewa: “Ina tababar cewa hanya daya ta tinkarar wannan ita ce ta kara saka bindigogi a makarantu. Kuma a tunani na mafi yawan Amurkawa na tababar cewa wannan ita ce hanyar da za ta warware ma na matsalar mu”.

A wani batu na daban kuma shugaban ya ce akwai wasu manyan matsaloli game da tabbatar da tsaro a ofisoshin jakadanci wadanda su ne su ka zama sanadin kisan da aka yiwa jami’an jakadancin Amurka hudu a Benghazi ranar goma sha daya ga watan satumba. Ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike a kan harin, amma ya ki amsa tambayar neman sanin wadanda jami’an gwamnatin Amurka su ka dorawa laifin kai harin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG