Shi ne tsohon shugaban babbar jam’iyar addinin kasar Pakistan ta Jamaat-e-Islami, shekaru ishirin da biyu ya yi, ya na shugabantar ta kafin ya yi murabus a shekarar dubu biyu da tara.
A watan nuwamban da ya gabata, Ahmed ya tsallake rijiya da baya, ya tsira ba ko kwarzane daga wani yunkurin neman yi mi shi kisan gilla lokacin da wani dan harin kunar bakin wake ya fasa boma-bomai daf da shi.
Ya na daya daga cikin manyan masu sukan lamirin yakin hadin guiwar Amurka da kungiyar kawancen tsaro ta NATO su ke yi a makwafciyar kasar Afghanistan.
Qazi Hussain Ahmed ya rasu da safiyar lahadi a Islamabad. Da ma shekara da shekarru ya na fama da cutar zuciya.