Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rage Hukumcin Da Za A Iya Yankewa Kan Manning


Firabiti Bradley Manning, a tsakiya, yana fitowa daga motar jami'an tsaro zai shiga kotu a Fort Meade, Jihar Maryland

Mai shari’a ta rage hukumcin da za a iya yankewa a kan sojan Amurka da ake tuhuma da satar mika bayanan sirri na Amurka ga kungiyar Wikileaks.

Wata mai shari’a ta soja a nan Amurka ta rage irin hukumcin da za a iya yankewa a kan wani sojan Amurka da ake tuhuma da laifin satar mika bayanan sirri na Amurka ga kungiyar nan ta Wikileaks.

Jiya talata mai shari’a Denise Lind ta yanke hukumcin cewa zata rage kwanaki 112 a kan duk wani hukumcin da za a iya yankewa a kan Bradley Manning a saboda yadda aka tozarta masa a wani kurkukun soja bayan kama shi.

Ana tsare da Manning tun tsakiyar shekarar 2010. A wasu lokutan, hukumomi sun killace shi shi kadai cikin dakin da ko taga babu na tsawon sa’o’I 23 kowace rana, wani lokacin ma tsirara.

Mai shari’ar ta yanke hukumci a lokacin zaman sauraron shaida kafin fara shari’ar cewa wasu daga cikin abubuwan da aka yi masa sun wuce kima, ko da gwamnati tana da damuwa ta zahiri kan wasu abubuwan. Amma kuma ta ce irin wannan musgunawa da aka yi masa ba ta kai ta yadda zata biya bukatun lauyoyi masu kare shi cewa a kori karar ba.

Manning yana fuskantar tuhume-tuhume 22, ciki harda “taimakawa abokan gaba” wanda hukumcinsa yana iya kaiwa daurin rai da rai. Za a fara shari’arsa a ranar 6 ga watan Maris.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG