Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Mura Tayi Karfi a Amurka


Cutar Mura
Cibiyar kare yaduwar cututtuka ta Amurka tace wannan shekara ce ta fi muni a yaduwar mura cikin shekaru 10 da suka wuce a nan Amurka, kuma har yanzu cutar bata kure karfinta ba.

An bada rahoton cewa cutar ta yadu cikin jihohi 44, kuma cibiyar tace kiyasin mutane da suke zuwa asibiti da alamun sun kamu da mura sun ninka sau biyu cikin watan da ya wuce. A wasu sassan na Amurka, asibitoci suna kin jinyar wadanda suka je da kukan mura.

A jiya laraba magajin garin birnin Boston ya ayyana dokar ta baci a fannin kiwon lafiya, inda aka sami kamar karin kaso 10 cikin 100 na mutane da suka kamu d a mura idan aka kwatanta da wadanda suka yi fama da wannan larura bara a cikin wannan birnin da yake arewa maso gabashin Amurka.

Hukumomin kiwon lafiya na Amurka sun ce cutar ta bullo wata daya kamin lokacinda ta saba bulla cikin watan Nuwamba, kuma cutar mai karfin H3N2, tana janyo larurar mai karfi, musamman ga wadanda suka manyanta.

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurkan tana bada shawarar ko mutane wadanda suke da shekarun haifuwa da ya haura wata shida su yi allurar riga kafin kamuwa da cutar ta mura. A shekarun baya bayan nan rigakafin yana aiki kashi 60-70 wajen hana kamuwa da cutar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG