Accessibility links

Sojojin Algeria Sun Kai Farmaki Akan Mayakan Sa Kai A Kamfanin Iskar Gas


Kamfanin Iskar Gas inda mayaka ke garkuwa da mutane. Photo Credit. AFP PHOTO/STATOIL/KJETIL ALSVIK
Sojojin Algeria sun kai wani farmaki a kan harabar kamfanin iskar Gas, inda mayakan sa kai masu alaka da al-Qaida suke garkuwa da mutane da suka kama jiya laraba.

Wani mai magana da yawun ‘yan mayakan yace an kashe akalla mutane 34 cikin wadanda ake garkuwa da su, da kuma ‘yan fashin su 15.

Babu wani cikakken bayani kan harin na yau. Kamfanin dillancin labarai na kasar Mauritania yace ya sami jimlar wadanda farmakin na yau ya rutsa da su ne daga daya daga cikin mayakan sakai dake harabar kamfanin.
Kamfanin dillancin labarai na kasar Aljeriya ya bada labarin cewa jiragen sama masu saukar ungulu su kai hari yayinda mayakan ke kokarin fita daga kamfanin tare da wasu daga cikin mutanen da suka kama. Mayakin da yayi magana da yawun ‘yan fashin, wanda bai bayyana ko shi waye ba, ya gaya wa kamfanin dillacin labaran cewa a kalla turawa guda 7 ne da ake garkuwa da su ke raye.

Ta wani gefen kuma, kamfanin dillacin labarai na Algeria, yace sojoji sun kwaci wasu ‘yan kasashen waje daga hannun mayaka. Rahotannin farko sun ce wadanda ake kwata da dan Kenya, ‘yan kasar Faransa guda biyu, da biyu daga Birtania.


Mayakan sakai masu kishin Islama wadanda suke da alaka da kungiyar al-Qaida sun bada labarin kama kimanin mutane 41 ‘yan kasashen ketare akamfanin jiya Laraba, mataki da mayakan suka ce ramuwar gayya ce kan matakin soja da Faransa ta dauka a makwabciyar kasar, watau Mali.

Wani kakakin kungiyar al-Qaida a yankin Maghreb reshenta dake Mali, ya gayawa Muryar Amurka cewa akwai Amurkawa cikin wdanda ake garkuwa da su. Jami’an Amurka sun gaskanta cewa akwai Amurkawa cikin wadanda ake garkuwa da su.

Sakataren tsaron Amurka Leon Panetta ya kira garkuwa da mutanen a matsayin ta’addanci.

Sauran mutanen da hannun mayaka sun hada da ‘yan kasashen Britaniya, Faransa, Japan, Norway da kuma Ireland.
XS
SM
MD
LG