Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al-Shabaab Ta Kashe Dan Kasar Faransa


Một nhân viên của Công ty ActiveLink biểu diễn áo robot ARM01 đồng chế tạo với Kubota Corp, tại Tokyo, Nhật Bản. ARM01 được chế tạo để giúp nông dân và công nhân xây dựng.
Kungiyar mayakan sakai al-Shebab dake Somalia ta bada labarin cewa ta kashe dan kasar Faransan nan da take garkuwa da shi fiye da shekaru uku.

A wani labari da ta saka a dandalin Twitter yau Alhamis, kungiyar tace tun jiya laraba ta kashe bafarnshen mai suna Denis Allex.

Jiya laraba al-shabab ta bada sanarwar niyyarta na kashe jami’in leken asiri na Faransan, wanda yunkurin da Faransa tayi na ceto shi cikin makon jiya ya faskara. Dama tuni jami’an kasar ta Faransa suka aza cewa jam’in da ake garkuwa da shi ya mutu.

Al-shabab tace ta dauki matakin ne domin abunda ta kira kashe farar hula da dakarun Faransa suka yi lokacin da suka kai somamen nema kubutar da jam’in kasar ranar jumma’a da ta shige, da kuma bayyana rashin amincewarta kan manufofin muzgunawa musulmi da Faransa take dauka, da kuma matakan sojin kasar a Faransa da kuma Afghanistan.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG