Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Da Tankokin Yaki Sun Zagaye Ma'akatar Gwamnati A Eritrea


Hoton yankin kasar Eritrea
Hoton yankin kasar Eritrea
Rahotanni dake fitowa daga babban birnin Eritrea, Asmara, sunce sojoji da tankokin yaki sun zagaye ma’akatar yada labarai bayan da sojojin masu tawaye suka kwace ginin.

Rahotannin sunce kimamin sojoji 100 ne suka kutsa ma ma’aikatar yau litinin, kuma suka tilastawa ma’aikatan gidan talabijin karanta wata sanarwar dake bukatar a saki dukkan fursunonin siyasa.

A wata sanarwar, ofishin jakadancin Britania a Eritrea yace ya samu rahotanni dake cewa akwai sufurin soji na ba saban ba, a birnin Asmara, kuma ofishin ya kara da cewa akwai alamun an rufe gidajen radio da talabijin na birnin.

Shugaban Eritrea, Isaias Afeworki yana gudanar da mulkin kama karya a kasar tun lokacinda ta samu ‘yan cin kai daga Ethiopia a shekara ta 1993.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG