Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta musamman dake bin bahasin laifukan yakin da aka tafka a rikicin kasar Saliyo, wadda kuma ke zamanta a birnin Hague, yau talata ta fara sauraren daukaka karar ta Charles Taylor.
Anji Lauyoyin Charles Taylor na yin kira ga kotun daukaka karar da ta share hukuncin da kotun farko ta yanke tare da rage karfin hukuncin domin yayi tsanani.
Amma lauyoyin gabatar da mai laifi gaban shari’a sun dage kan sai kotun ta bar hukuncin farko domin laifukan da Charles Taylor ya aikata sun wuce gaban mai hankali.
Idan dai za’a tuna, a watan Afrilun shekarar 2012 ne kotun farko ta yankewa Charles Taylor hukuncin daurin bayan da ta sameshi da laifuka har goma sha daya na wulakanta mutuncin Bil Adama tare da goyon bayan mayakan ‘yan tawayen Saliyo da samar masu tulin makamai.