Jakadan Ivory Coast a Majalisar Dinkin Duniya Yusuf Bamba, wanda har ila yau shine wakilin ECOWAS a majalisar, ya ce tuni kamar sojoji dubu daya daga yankin sun isa Mali. A jiya talata ya sake kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta samarda gudumawar kudi na gaggawa da kuma wasu kayan aiki domin taimakawa matakin sojin da aka dauka.
Dakarun faransa da na Mali sun takawa mayakan sakan birki, wadanda suka fara dannowa ta kudancin kasar, bayanda suka kama kusan arewacin kasar baki daya, a bayan da sojojin Malin suka ayyana juyin mulki cikin watan Maris na bara.
Wakilin Muriyar Amurka a Gao yace galibin mayakan sakai dake can sun arce daga birnin tun cikin makon jiya lokacinda jiragen yakin Faransa suka fara kaiwa sansanonin mayakan sakan harin bama-bamai.