Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tsageran Somalia Na Barazanar Kashe 'Yan Kenya


Dakarun Al-shabab kenan a kan motar a kori kura. 8/12/2012
Dakarun Al-shabab kenan a kan motar a kori kura. 8/12/2012
Wasu ‘yan tsagera na kasar Somalia suna barazanar cewa zasu fara karkashe wasu ‘yan kasar Kenya daga hannunsu muddin gwamnatin Kenya din bata sako wasu Musulmi dake tsare a hannunta ba.

A jiya Laraba ne kungiyar ‘yan tsagera ta al-Shebab suka sako wani faifan bidiyo dake nuna wasu ‘yan Kenya da suka ce suna rike da su.

A cikin faifain ne aka ga daya daga cikin wadanda aka kama din, Mule Yesse Edwards, yana rokon jami’an Kenya har ma da ‘yan takaran shugaban kasa da suyi iya kokarinsu, su tabo su daga wannan kangin.

Haka kuma a cikin sakkonin Twitter masu dama da tayi ta aikawa, kungiyar ta al-Shebab tayi ta nanata cewa lalle hukumomin na Kenya suyi abinda take nema daga yanzu zuwa ran 14 ga watan Fabrairu mai zuwa, in ba haka ba kuwa, zata kashe wadanan mutanen.

Bukatocin al’Shebab din sun hada da neman a sako dukkan fursunoni Musulmi dake tsare a hannun Kenya da kuma sako Musulmin da aka aika zuwa Uganda don su fuskanci shara’oi kan laifukkan ta’addancin da ake zarginsu da aikatawa.

A cikin watan Oktobar 2011 ne dai Kenya ta tura sojoji zuwa cikin Somalia don su yaki dakarun al-Shebab wadanda suka jima suna tsallakowa zuwa cikin Kenya, suna kama mutane, suna garkuwa da su.
XS
SM
MD
LG