Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Turai Sun Gargadi Mutanensu Dake Birnin Benghazi


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton a lokacin da take ganawa da 'yan majalisar wakilan Amurka domin fadin abinda ta sani dangane da harin Benghazi
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton a lokacin da take ganawa da 'yan majalisar wakilan Amurka domin fadin abinda ta sani dangane da harin Benghazi
Jami’an gwamnatocin kasashen Ingila, Jamus da Netherlands sun gargadi mutanensu dake zaune a birnin Benghazi na kasar Libya da cewa suyi sauri su fice daga garin bayan wata sanarwar da aka bada na nuna cewa ana dab da soma kai hare-haren akan mutanen kasashen Yammacin Turai.

Ministocin harakokin wajen kasashen uku ne suka bada wannan jan kunnen yau Alhamis, inda har na Ingila ya nuna cewa ana sa ran a kai wasu daga cikin hare-haren akan wuraren da aka san turawan yammaci na yawan zuwa.

Wannan gargadin yana zuwa ne kwana daya bayanda sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton ta bada sheda a gaban majalisar dokokin Amurka kan farmakin da aka kai ran 11 ga watan Satumbar bara akan karamin ofishin jakadancin Amurka dake can Benghazi, inda a ciki har aka kashe jakadan Amurka Christopher Stevens da wasu Amurkawa ukku.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG