Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar Bam Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane Takwas A Syria


Wani mayakin 'yan tawaye akan hanyarshi a gaban wani gini da sojojin gwamnati suka fasa a unguwar Mleha dake birnin Damascus Junairu 21, 2013.
Tagwayen fashewar bam din mota a yankin Tuddan Golan, bangaren rikon ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8 yau jumma’a yayinda dakarun gwamnatin suka kaddamar da sabon samame a yankin Damascus da yan tawaye suka kwace.

Kungiyar kare hakkin yan adam ta Syria ta Observatory ta ce yawancin wadanda suka mutu a fashewar bam din na Golan sojojin leken asiri na Syria ne.

Har Yanzu ba a sami wanda ya dauki alhakin harin ba , duk da cewar sanya bam da harin kunar bakin wake wata dabara ce da mayakan ‘yan kishin islama ke amfani da ita suna yakar dakarun Syria, a yayinda su da ‘yan tawayen ke kokarin hambare shugaba Bashr al-Assad.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG