Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Iraki Sun Bude Wa Masu Zanga-zanga Wuta


Masu zanga-zanga kennan a lokacin da suke jifar dakarun Iraki da duwatsu a garin Falluja dake Iraq, January 25, 2013.
Jami’ai sun ce dakarun Iraki sun kashe akalla 'yan zanga-zanga uku, da yawa kuma sun raunata a birnin Fallujah.

'Yan sandan sun ce 'yan zangazangar suna kan hanyar hadewa da 'yan adawar gwamnati a wani gangami da aka yi a gabashin Fallujah yayinda sojojin suka tare hanyar su.

Ganin haka ya sa yan zanga-zangar suka fara jifar dakarun da abubuwa, wanda ya sa su kuma dakarun suka bude masu wuta.

Kafofin assibiti sun tabbatarda mutuwar mutane 3.

'Yan zanga-zangar mazhabar sunni ne suka fara dunguma kan titunan yammacin lardin Anbar a watan da ya gabata a zanga-zangar da suka yi akan firayim minister Nouri al-Malik da mulkin 'yan shi’a a Iraki, wanada suka ce yana danne bukatocin ‘yan darikar su.
XS
SM
MD
LG