Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

232 Sun Mutu,100 Sun Ji Ciwo A Gidan Rawar Brazil


'Yan kwana-kwana na kokarin kashe gobarar da ta lankwame rayukan mutane 232 a wani gidan rawa a Santa Maria
'Yan kwana-kwana na kokarin kashe gobarar da ta lankwame rayukan mutane 232 a wani gidan rawa a Santa Maria

A cewar hukumomi da asubahin jiya lahadi gobarar ta tashi a wannan gidan rawa da ake kira Kiss

Jami’an Brazil sun ce mutane 232 sun mutu, wasu fiye da 100 kuma sun ji rauni a bayan da gobara ta tashi cikin wani gidan rawa da ya cika makil da daliban jami’a a birnin Santa Maria dake kudancin kasar.

Hukumomi sun ce gobarar ta tashi da asubahin jiya lahadi a wannan gidan rawa da ake kira Kiss. Wadanda suka kubuta da rayukansu, sun ce wani daga cikin makida dake wasa a lokacin, shi ne ya kunna wani abin wasan wuta mai kama da Knockout ya cilla shi sama a dakin da suke wasa.

Da yawa daga cikin wadanda suka mutu, sun suke ne, ko kuma dai an tattaka su a lokacin da mutane ke kokawar fita daga cikin wannan gidan rawa.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yace yana jimamin wannan bala’i, musamman ma ganin cewa matasa da dalibai masu yawa haka sun mutu. Ya aike da sakonsa na ta’aziyya ga iyalan mamatan.

Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef, ta tsinke ziyarar da take yi a kasar Chile ta koma gida a jiya lahadi a bayan wannan gobara.

Santa Maria birni ne dake da babbar jami’a da kuma mutane kimanin dubu 250. Birnin yana kuryar kudancin Brazil a kusa da inda ta yi iyaka da kasashen Argentina da Uruguay.
XS
SM
MD
LG