Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Aika Biri Sararin Subahana


Iran ta aika biri sararin subahana
WASHINGTON, D.C. -- Kasar Iran tace tayi nasarar aika biri zuwa sararin subahana.

Ministan tsaro Ahmad Vahidi ya gayawa gidan talabijin din gwamnati cewa birin ya dawo da ransa bayan yayi tafiyar nisan kilomita 120 cikin sararin subahana a cikin wani kumbo.

Rahoton bai bada karin bayani ba akan lokacin da aka aika wani biri, da kuma wajen da aka gudanar da hakan. Yunkurin Iran domin saka biri a samaniya na karshe bai yi nasara ba a shekara ta 2011 saboda dalilan da basu fada ba.

Shirye-shiryen Iran dangane da fasahar sararin subahana na matukar damun kasashen yammacin duniya, saboda suna tsoron Iran din zata iya amfani da rokokin da take hadawa domin daukar makaman kare dangi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG