Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Garin Kidal Ya Kubucewa 'Yan Tawayen Kasar Mali


Wani sojan kasar Faransa cikin damarar yaki ya na gadin filin jirgin saman Timbuktu

Sojojin kasar Faransa sun kwace garin Kidal a saukake ba wata turjiya daga mayakan Islama

Dakarun kasar Faransa sun kwace iko da filin jirgin saman Kidal, wanda shi ne wuri na karshe da ya rage a hannun mayakan Islama wadanda su ka karbi iko a arewacin Mali bara.

Dakarun kasar Faransa sun fadi jiya Laraba cewa sojoji sun kwace filin jirgin saman da daddare. Haminy Maiga Shugaban Babbar Majalisar Yankin Kidal, ya ce sojojin sun iso ne ta jirgin sama da jirage masu saukar ungulu, kuma basu gamu da wata turjiya ba yayin da su ka diro.

Kungiyar Azbinawa wadda babu ruwanta da addini, MNLA a takaice ta fadi a farkon wannan satin cewa mayakanta sun kwace Kidal daga kungiyar Islama ta Ansar Dine.

Maiga, wanda ke tattaunawa da mutanen garin ta wayar da ke amfani da tauraron dan adam (ko satellite) ya ce kungiyar MNLA a yanzu ta na can gefe-gefen garin kuma mayakan Ansar Dine sun gudu zuwa kauyukan da ke kusa da wurin.

A halin da ake ciki kuma, galibin tsoffin kasidun tarihi da ke birnin Timbuktu na kasar Mali na nan daram.

Magajin garin ya ce masu kaifin kishin Islaman sun cinna wuta a Cibiyar Ahmed Baba, wanda wani babban dakin karatu ne, a yayin da su ke tserewa daga garin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG