Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Kamalla Aikin Kwato Mali Daga 'Yan Tawaye


Ministan tsaron Faransa kennan, Jean-Yves Le Drian a lokacin da yake daukan hoto da sojojin Faransa a sansanin Miramas, dake kudancin Faransa. Junairu 25, 2013.
Wani babbar kusar gwamnatin Faransa yace sun kamalla aikin kwato kasar Mali daga hannun ‘yantawaye a cikin “nasara”, amma fa yana jan kunnen cewa dole ne bangarorin kasar masu jayayya da juna su shirya a tsaianinsu – ko a koma ‘yar gidan jiya.

A yau Alhamis ne ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian yake wannan kalamin a daidai lokacinda shi kuma shugaban kasar Malin na rikon kwarya, Dioncunda Traore yake yanke kaunar duk wata tattaunawar sulhu da ‘yan kishin Islaman dake wannan tawayen, wadanda kuma suka cafke yankin arewancin kasar.

Da yake magana da wata tashar rediyon Faransa, ministan yace sun gama cika aikin da shugaban kasarsu Francois Hollande ya basu na hana wa ‘yantawayen Mali din kutsawa zuwa cikin kudancin kasar.

Yace yanzu Faransa tana aiki da jagabannin Mali da na kasashen Afrika don maido wa Mali cikakken ‘yancinta da martabarta, abinda yace wani abu dake tafiya a cikin hanzarin da wasu basu yi tsammani ba.
XS
SM
MD
LG