Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Barin Shedu Komawa Gidan Discon Da Gobara Ta Kama


Gidan holewan da gobara ya kama kennan.
‘Yan sandan birnin Santa Maria na kasar Brazil sun soma barin wasu shedu su koma cikin kulob din nan da rawar ‘yan Disco inda kwanan baya gobara ta tashi, har ta lakume rayukkan mutane 235.

Bayanda suka binciki wurin ne ‘yansanda suka yanke hukuncin cewa wutar ta taso ne daga wani sashe na kulob din inda ake yi tarwatsi wuta don holewa.

Wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu sunce daya daga cikin makadan disco ne ya bartsatsa wutar zuwa ga silin din rufin wurin, wanda ya kama wuta, kafin a ankara kulob din duk ya kama, hayaki ya sunke kowa.

Barnar ta karu da yake ba wani tanadin mafitar gaggawa da ake da ita a gidan, ‘yar abar kashe wuta da ake da ita bata aiki, sannan kuma ‘yar kofa daya tilau da ake da ita ta fita, an toshe ta.

Lokacinda wannan gobarar ta tashi, kulob din shake yake da dubban matasa, wadanda da yawansu shakewa suka yi daga hayaki, suka mutu, wasu kuma tattaka su aka yi, suka hallaka.
XS
SM
MD
LG