Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeria Ta Doke Mali 4-1


Nigeria soccar players celebrate a goal against Mali. Wednesday, 6th Febuary 2013 (Reuters)
WASHINGTON, DC -- A karo na farko a shekaru 13, kungiyar kwallon kafan Najeria zata buga wasan karshe a gasar kofin nahiyar Afirka da akeyi a Afirka ta Kudu, bayan doke kungiyar kwallon kafar Mali a wasan kusa da karshe da ci 4 da 1.

Dan baya Elderson Echiejile ne ya fara jefa kwallo a raga, minti 25 da sa wasa bayan wata kwana da Victor Moses ya aika. Bayan minti biyar kuma, Brown Ideye yayi arangama da mai kare ragar Mali, Mamadou Samassa a inda ya jefa kwallo na biyu a ragar Mali.

Ci na uku kuwa, wani kwallon free kick da Emmanuel Emenike ya doka saura minti 3 a je hutun tsakar wasa ne ya daki kafar Momo Sissoko na Mali, ya canza hanya kana ya shiga raga. Ci na karshe ya zone daga Ahmed Musa bayan minti 60 da fara wasa, sannan Mali din ta ramo ci daya yayinda Cheick Diarra ya jefa kwallo a ragar Najeria minti 15 bayan cin da Musa yayi.

Nasarar wannan wasa ya baiwa kungiyar Super Eagles din na Najeria damar karawa da duk wanda ya ci wasa tsakanin Ghana da Burkina Faso.

Kwallon kafa a Najeria ya kasance tsin-tsiyar dake daure 'yan kasar baki daya. A duk lokacin da Najeria tayi nasara, mutane suna girke bam-bamce bam-bamcensu a gefe daya domin nuna farin cikinsu a matsayinsu na 'yan Najeria baki daya. Misalin wannan nasara itace ta gasar wasannin motsa jiki a turance Olympics, da akayi a shekara ta 1996, fagen da Najeria ta doke goggagun kasashe masu tarin fitattun 'yan kwallon kafa kamar Brazil da Argentina.

Rabon Najeria da buga wasan karshe a wannan gasa tun shekara ta 2000 a inda kasar Cameroon tayi nasara a bugun fenariti da ci 4 da 3. Sau biyu Najeria tana cin kofin a wasan karshe, a shekara ta 1980 a gida Najeria, da kuma 1994 a Tunisia.

Za'a doka wasan karshe ran 10 ga Fabrairu a filin wasa na FNB dake birnin Johannesburg.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG