Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyun Adawa A Najeria Sun Hada Kai Sun Zama APC


Hoton dan takarar tsohuwar jam'iyyar CPC kennan, Janar Muhammadu Buhari.
Hoton dan takarar tsohuwar jam'iyyar CPC kennan, Janar Muhammadu Buhari.
WASHINGTON, DC -- Jam'iyyun Adawa guda hudu a Najeria, wato CPC, ACN, ANPP da APGA sun hada kai sun zama sabuwar jam'iyya guda daya mai suna All Progressives Congress ko APC a takaice.

A taron da aka shafe kwana biyu ana yi a birnin tarayyar Najeria, Abuja, wakilan jam'iyyun sun yanke wannan shawara domin fuskantar zaben shekara ta 2015. Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tuntubi daya daga cikin wakilan, Senata Hadi Sirika na jihar Katsina.

"Lokaci yayi da jam'iyyun adawa zasu hada karfi da karfe domin tunbuke wannan jam'iyya mai mulkin Najeria tsawon shekara 12, wadda ta durkusar da al-amuran kasar, da suka shafi tattalin arziki, da zamanta kewa, da tsaro", a cewar Senata Hadi Sirika.

Senata Sirika ya kara da cewa taron da aka kamalla a yammacin yau ya hada wani kwamiti da zai shigar da takardun jam'iyya ga hukumar zabe ta Najeria.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG