A cikin shafinsa na duniyar gizo ta internet, Ayatollah Ali Khamenei ya fada cewa Amurka na neman a zauna ayi magana amma kuma tana yiwa Iran barazanar kai mata hari, abinda yace ba zai taba razana Iran ba.
Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ne ya tado da maganar a jawabin da yayi wa wani taron harkokin tsaro a birnin Munich na Jamus, inda yake cewa a shirye Amurka take ta zauna tayi tattaunawar kai tsaye da Iran idan Iran din da gaske take son a warware wannan cece-kucce.
Kalaman Ayatollah Khamenei dai suna zuwa ne kwana daya bayanda aka fara aiwatarda wani sabon matakin da Amurka ta fito da shi na auna masana’antun man fetur na Iran da niyyar karya su.