Accessibility links

Shugaba Chavez Na Yin Wata Jinya Ta Daban Mai Wuya

  • Halima Djimrao-Kane

Mataimakin shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro, ya na yin bayanin halin da shugaba Hugo Chavez ya ke ciki a kasar Cuba

Mataimakin shugaban kasar Venezuela ya ce shugaba Hugo Chavez na cikin wata jinya mai sarkakkiya a kasar Cuba

Mataimakin shugaban kasar Venezuela y ace shugaba Hugo Chavez ya na yin wata jinya ta daban mai wuya bayan tiyatar karshen da aka yi mi shi a kasar Cuba saboda cutar sankara ko ciwon daji.

Mataimakin shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro bai yi dalla-dalla ba a jiya laraba da yake bayar da sabon bayanin halin da shugaba Hugo Chavez ya ke ciki.

Watanni fiye da hudu kenan ba a ga Mr.Chavez a bainar jama’a ba, kuma jami’an gwamnatin shi ba su bayar da wani isasshen bayani ba game da rashin lafiyar shi ko kuma halin da yake ciki. Sun dai ce ya na da ciwon daji a wajejen kwatangwalon shi.

Sau hudu ana yiwa shugaba Hugo Chavez tiyata saboda cutar sankara. A watan jiya bai samu halartar bikin rantsar da shi a wa’adin mulki na hudu ba.

Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez wanda ke fama da cutar sankarar da yake jinya a kasar Cuba
Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez wanda ke fama da cutar sankarar da yake jinya a kasar Cuba
XS
SM
MD
LG